Tsohon Shugaban Kasa Ya Bukaci Shugabanni Su Yi Koyi da Marigayi Yar'adua

  • Yayin da marigayi Umaru Musa Yar'adua ya cika shekaru 14 da rasuwa, Janar Yakubu Gowon ya yabawa salon mulkinsa
  • Tsohon shugaban kasar ya ce Yar'adua ya na da kyakkyawar zuciya kan Najeriya da 'yan kasar duba da irin tsare-tsarensa
  • Gowon ya bayyana haka a jiya Litinin 6 ga watan Mayu a Abuja yayin taron tunawa da tsohon shugaban kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya yabawa salon mulkin marigayi Umaru Musa Yar'adua.

Yakubu Gowon ya ce idan da Yar'adua ya kammala mulkinsa da yanzu Najeriya ta wuce yadda ta ke.

Janar Gowon ya ƙoda marigayi Yar'adua

Kara karanta wannan

"Da yawa ba su da muƙamai": Jigon APC ya magantu kan zargin rikicin Tinubu da El-Rufai

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin babban taro kan Yar'adua da aka gudanar a ranar Litinin 6 ga watan Mayu, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Yar'adua ya cimma abubuwa da dama a kasar wanda ya kawo zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

Daga cikin abubuwan kamar yadda Gowon ya tabbatar akwai afuwa ga tsagerun yankin Neja Delta da ke Kudancin Najeriya, TheCable ta tattaro.

Gowon ya jero alheran shugaba Yar'adua

"Mutum ne mai gaskiya da rikon amana, ya yi abubuwa masu kyau wanda ya kamata a rinka tunawa da shi.""Ya kasance mai gaskiya ganin yadda ya yi korafi kan yadda ya samu mulki, ya kafa kwamiti amma bayan rasuwarsa aka yi watsi da binciken.""Ya kasance mai gaskiyar, bai saci komai ba, ba ka isa ka kama shi da sata ba, ya yi afuwa ga tsageran Neja Delta domin kare arzikin kasa."

Kara karanta wannan

Attajiri ya bukaci 'yan Najeriya su marawa Tinubu baya, ya fadi lokacin samun sauyi

- Yakubu Gowon

Gowon ya ce Yar'adua ya so Najeriya

Gowon ya ce tabbas Yar'adua yana da kyakkyawar zuciya ga Najeriya inda ya shirya tsamo ta a ƙangin da ta shiga.

"Rashin lafiyarsa da mutuwarsa, na yi imani idan da Ubangiji ya ba shi tsawon rai, da Najeriya ta samu ci gaba sosai kuma ta yi kyau."

- Yakubu Gowon

Tambuwal ya yabawa marigayi Yar'adua

A wani labarin yayin da ake tunawa da marigayi Umaru Musa Yar'adua, an ji Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya yabawa tsohon shugaban kasar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Yar'adua a ranar 5 ga watan Mayun 2010 bayan fama da jinya a kasar Saudiyya.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbn5zgZZmsJqmkWKxonnGmqqkoamWerW%2FzqGmp2WjncKorcGapWajkaiubsXAZpmuo5GYtm6%2Fx66empqRo7uqedKuZLKhXaC8urWMnZhmpZGntqit2KJkspmilrG2rY4%3D