- Fitattun mawakan Najeriya, Ayodeji Balogun da David Adeleke sun sake gwabzawa yayin suke ci gaba da gasa
- Mawaki Wizkid ya yi shagube ga Davido a shafinsa na X inda ya ke sukarsa kan wani faifan bidiyo da ya wallafa
- Daga bisani Davido ya yi martani mai zafi inda ya ce ya yi da-na-sanin kokarin taimakonsa a baya saboda ci gabansa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Alaka na ƙara tsami tsakanin fitattun mawakan kudancin Najeriya, Ayodeji Balogun da David Adeleke a kwanakin nan.
A daren jiya Litinin mawaki David Adeleke da aka fi sani da Davido ya rinjaɓe da Ayodeji Balogun da aka fi sani da Wizkid wanda ya ɗauki hankali a kafofin sadarwa.
Tsohon ma'aikacin CBN ya fallasa yadda ya karbowa Emefiele cin hancin Dala 600,000
Musabbabin rikicin Wizkid da Davido
Rikicin ya fara ne bayan Wizkid ya yi shagube ga fitaccen mawaki Davido a shafin X wanda aka fi sani da Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mawakin ya caccaki Davido kan wani faifan bidiyonsa ya durkusa ya na addu'a da kuma kuka bayan wani mai goyon bayansa ya roke shi ya sake sabuwar waka.
Wallafar mawakin ta dauki hankalin mutane da dama a kafafon sadarwa inda suke tambayar mene damuwar mutanen biyu.
Daga bisani, Davido ya yi martani mai zafi wanda ya wallafa a shafukan sadarwa kan mawaki, Wizkid.
"Yanzu kam babu wanda ya san wadannnan shirmen wakokin naka."- Davido
Davido ya watsawa Wizkid baƙar magana
Davido ya ce mutane da dama yanzu sun bar sauraron wakokinsa inda ya ce Wizkid ya rasa magoya bayansa.
Wizkid ya yi gaggawar mayar da martani a shafin X ga Davido inda ya ce suna bukatar addu'a.
Majalisar Dattawa Ka Iya Sake Nazari Kan Dakatar da Sanatan Bauchi, Bayanai Sun Fito
"Kun san meye, babu komai, rikitattun mutane kuna neman addu'a, ina muku addu'a."- Wizkid
Davido daga bisani ya sake martani da kiran Wizkid a matsayin marar lafiya inda ya ce ya yi da-na-sanin niyyar taimakonsa a baya.
Fitacciyar mawakiyar yabo ta rasu
A wani labarin, kun ji cewa wata matashiyar mawaƙiyar yabon addinin Kirista, Morenikeji Adeleke ta riga mu gidan gaskiya.
Marigayiyar ta rasu ne a ranar Asabar 27 ga watan Afrilu inda aka bayyana ta a matsayin mace mai taimakon jama'a.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC51K2Yp51fZoJ6fJFqbGamkWLGqnnDmqWaZaOWu6p5xaKrmqykqrtuucCwmKSZnmK7orbEq6CymV1nerTBzWaesJmSr65uxcCyoKdllJZ6orjApJhmo5ViuKK%2BwGarrJmdnnq1v8CkmKehnqjCcA%3D%3D